HRW: Sojojin Itopiya sun kashe fararen hula 83 a Tigray

HRW: Sojojin Itopiya sun kashe fararen hula 83 a Tigray

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana cewar, sojojin Itopiya sun kashe fararen hula 83 a yankin Tigray tun farkon fara kaiwa 'yan tawaye hare-hare zuwa yau.

Daraktar HRW a yankin Kahon Afirka, Laetitia Bader ta sanar da cewar, tun watan Nuwamban 2020 da Itopiya ta fara kai hare-hare a Tigray, ta lalata makarantu, gidaje da asibitoci inda ta kuma kashe fararen hula 83 da suka hada da yara kanana.

Ta ce "Hare-haren sun yi daidaita fararen hular Tigray, an kuma tilasta musu yin gudun hijira."

HRW ta ce, sama da mutane dubu 200 ne suka gudu daga Tigray tare da neman mafaka a Sudan.

Bader ta yi kira ga gwamnatin Itopiya da ta bayar da dama ga masu sanya idanu na Majalisar Dinkin Duniya su gudanar da nazari a Tigray.


News Source:   ()