Hatsarin jirgin sama ya kashe fararen hula da sojojin Sudan sama da 40

Hatsarin jirgin sama ya kashe fararen hula da sojojin Sudan sama da 40

Babban kwamandan Sudan Manjo Janar Bahr Ahmed na cikin mutanen da hatsarin ya rutsa da su, kamar yadda hukumomin ƙasar suka tabbatar.

Jirgin na Antonov ya faɗi a daren Talata kusa da sansanin sojin sama na Wadi Seidna, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin soji a Omdurman da ke arewa maso yammacin babban birnin kasar.

Rundunar sojin da ke yaki da ‘yan tawayen RSF tun a watan Afrilun 2023, ta ce jirgin ya yi hadari ne a lokacin tashinsa, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an soji da fararen hula.

Ma'aikatar tsaron ƙasar ta fitar da sanarwar cewa, tuni aka tura tawaga ta musamman domin kai ɗaukin gaggawa, inda aka garzaya da waɗanda al’amarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, matsalar na’urar da aka samu, shine ita ce musabbabin hatsarin jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)