Hatsarin jirgin ruwa a Najeriya ya yi ajalin fasinjoji 21

Mutane 21 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa a Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewar jirgin ruwan dauke da fasinjoji da kaya da yawa ya kife a kogin Benue.

An bayyana mutuwa mutane 11 a hatsarin yayinda ake nemi wasu da dama aka rasa.

Kakakin 'yan sandan Benue Catherine Anene ta bayyana cewar an kubutar da mutane 2 a aikin ceto da aka gudanar a yankin.

Anene ta ce ana ci gaba da neman mutanen da suka bata a kogin.


News Source:   www.trt.net.tr