Hatsarin jirgin ruwa a Mozambik

Hatsarin jirgin ruwa a Mozambik

Mutane 40 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa dauke da fasinjoji a kogin jihar Cabo Delgado na kasar Mozambik.

Majiyoyin yankin sun bayyana cewar jirgin ya tashi dauke da fasinjoji 74 daga garin Palma da ke iyakar Mozambik da Tanzaniya, kuma ya kife a kusa da Tsaunin Ibo.

A kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu inda aka kubutar da wasu 32.

An samu labarin cewar jirgin ya kife saboda diban mutane sama da yadda ya kamata, kuma mutanen sun gujewa rikicin da ake yi a arewacin Mozambik.

Sojojin Mozambik na kai hare-hare kan wasu 'yan bindiga da suka bulla a jihar Cabo Delgado shekaru 3 da suka gabata.

Jihar na da yawan albarkatun kasa da na iskar gas kuma tana da yawan mutane miliyan 2,3.


News Source:   ()