Hatsarin jirgin kasa ya yi sanadiyar rayukan mutum 33 a Misira

Hatsarin jirgin kasa ya yi sanadiyar rayukan mutum 33 a Misira

An sanar da cewa hatsarin jirgin kasa a yankin kudancin Misira ya yi sanadiyar rayukan mutane 33 inda wasu 66 suka raunana.

Kamar yadda ma'aikatan lafiyar kasar ta sanar, a garin Tahta dake karkashin Suhac dake kusa da rafin Nil jiragen kasa biyu sun yi karo da juna.

An bayyana cewa mutum 33 sun rasa rayukansu inda wasu 66 suka raunana sakamakon taho mu gaman da jiragen kasan suka yi a Misira.

An dai fara bincike akan lamarin da ya haifar da kaucewar jiragen daga layin dogo.

An dai bayyana cewa ana yawan samun hatsarin jiragen kasa sabili da tsofan da layin dogon kasar Misira suka yi.

A ranar 9 ga watan Disamban 2020 ma an samu hatsarin jirgin kasa da ya yi sanadiyar rayukan mutane 22.

 


News Source:   ()