Harin 'yan tawaye ya yi ajalin sama da mutum 200 a kudancin Sudan

Harin 'yan tawaye ya yi ajalin sama da mutum 200 a kudancin Sudan

Daga ayyukan ta’addancin da ‘yan tawayen RSF suka ƙaddamar kan fararen hular Sudan din, akwai kisa, garkuwa, fyade da sauran laifukan da suka danganci cin zarafi, kamar yadda rahoton wata ƙungiya da ke bibiyar laifukan keta haddin ɗan adam.

Rahoton kungiyar ya ci gaba da cewa, ‘yan tawayen sun yi ta harbin mutane, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa hare-haren su, inda suka rika tsallakawa ta Kogin Nilu, har ta kai ga da dama suka nutse a ruwa.

Kungiyar ta ce, wannan aikin ta’asa bashi da maraba da aikata laifukan yaki, yayin da aka dauki tsawon watanni 21 ana cikin tashin hankali a kasar da ke arewa maso gabashin Afirka.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar ta ce, adadin mutanen da suka mutu ya tasamma 433 ciki kuwa har da jarirai.

Rahotanni sun ce gomman mutane ne suka mutu a ranar litinin kaɗai, sakamakon munanan hare-haren da ‘yan tawayen na RSF suka ƙaddamar.

Waɗannan hare-hare na zuwa ne, bayan sanarwar da gwamnatin Sudan ta fitar da ke cewa, ta samu nasarar kakkabe duk wani burbushin ‘yan tawayen RSF, a ciki da wajen birnin Khartoum.

A makon jiya ne, gwamnatin sojin kasar, ta sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya, a matsayin wani shiri na musamman da zai kawo karshen mulkin soji da kuma yaƙin da ake yi a cikin ƙasar.

Sai dai a wannan makon ne ‘yan tawayen tare da wasu kungiyoyi, ake sa ran za su yi zama na musamman a Nairobi, kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa, domin kafa gwamnati a yankunan da ke karkashin ikon RSF ɗin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)