Harin ƙunar baƙin wake ya hallaka mutane 32 a Mogadishu na ƙasar Somaliya

Harin ƙunar baƙin wake ya hallaka mutane 32 a Mogadishu na ƙasar Somaliya

Ƴan sandan ƙasar sun tabbatar da harin na ranar Jumma'a wanda ke zama ɗaya daga cikin mafi muni da aka kai ƙasar da ke gabashin Afirka cikin watannin baya bayan nan.

Sama da shekaru 17 mayakan masu ikirarin jihadi da ke da alaka da Al-Qaida ke ƙaddamar da hare-hare kan muradun gwamnatin tarayya da ke samun goyon bayan kasashen duniya, kuma a baya bayan nan sun kai hari a yankin gabar tekun Liido, wanda ya shahara da ‘yan kasuwa da jami’ai.

Wani bidiyon da ba a tantance ba da aka yaɗa ta yanar gizo bayan harin da aka kai a yammacin ranar Juma'a, ya nuna yadda mutane ke tserewa a kan titi, yayin da ake ganin gawarwaki cikin jini a bakin gabar teku.

Al- Shabaab ta ɗauki alhaki

Harin wanda kungiyar ta Al-Shabaab ta ɗauki alhakinsa a wani sako da ta wallafa a shafinta na yanar gizo na masu goyon bayan al-Shabaab, ya fara ne lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da na’urar, yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta nan take kan mai uwa da wabi.

da lokacin da fashewar ta auku, inda suka bayyana yadda ‘yan bindigar suka far wa yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)