Harin ta'addanci ya kashe sojojin Burkina Faso shida a arewacin ƙasar

Harin ta'addanci ya kashe sojojin Burkina Faso shida a arewacin ƙasar

Majiyoyin cikin gida sun ruwaito cewa, maharan su na da yawa kuma suna ɗauke da muggan makamai, inda suka nufi wuraren da sojoji ke aikin sintiri.

Wannan harin kwantan bauna dai, rundunar sojin kasar ta ce ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla sojojin Burkina Faso shida.

Duk da ƙazamin fadan da aka yi, maharan sun yi nasarar tserewa, inda suka tafi da kayayyakin yaƙi masu daraja.

Tun shekaru uku da suka gabata, aka yi wa garin ƙawanya, inda mazauna garin ba sa iya fita ko shiga ba tare da kariyar sojoji ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)