Harin ta'addanci ya kashe sojoji da fararen hula sama da 100 a Burkina Faso

Harin ta'addanci ya kashe sojoji da fararen hula sama da 100 a Burkina Faso

Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mazauna garin ke ƙoƙarin  taimaka wa jami’an tsaro wajen gina ganuwar  da za ta samar da kariya ga shingen tsaro, inda ƴan bindigan suka buɗe musu wuta, lamarin da ya rutsa da kimanin mutane 100 nan take.

Majiyoyin tsaro da dama sun ce ɗimbim sojoji sun bace a  cikin wannan ribibi, kuma maharan sun yi awon gaba da tarin makamai har da motar ɗaukar marasa lafiya ta sojoji.

Mutane da dama ne suka jikkata a wannan  hari, inda akalla 140 daga cikin su ne aka garzaya da su cibiyoyin kula da lafiya a yankin.

An kira dukkannin ma’aikatan da ke aiki a ɓangaren tiyata a garin Kaya na tsakiyar Burkina Faso don taimakawa wajen kula da waɗanda aka fara kai su asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)