Harin ta'addanci ya kashe jami'an wata ƙungiyar agaji ta Switzerland

Harin ta'addanci ya kashe jami'an wata ƙungiyar agaji ta Switzerland

Kungiyar ta ce al’amarin ya rutsa da su lokacin da suke tsaka da aikin bayar da agaji a Rutshutu, mai tazarar kilomita hamsin tsakanin sa da arewacin birnin Goma da ya fada karkashin ikon ‘yan tawayen a makon jiya.

Sai dai kungiyar bata bayyana wadanda ke da alhakin mutuwar jami’an nata ba, amma dai ta ce tana gudanar da bincike a kai.

Ƙungiyar agajin da aka fi sani da HEKS/EPER, na dauke da kaso mai yawa na aikin agajin da ake gudanarwa a gabashin Congo da ma yankunan da ke fama da rikicin masu dauke da makamai.

A halin yanzu dai, ƙungiyar ta ce ta dakatar da ayyukanta a wannan yanki, har sai baba ta gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)