Haren haren wadanda kungiyar Jnim dake mubaya’a ga al’Qaida ta dauki alhakin kaisu sun shafi Gariruwan Bourari, Madina, Gasa, Massassegue, Sounfounou da kuma Irguelou da tsaka rana jiya juma’a.
Majiyoyi daga yankunan da lamarin ya auku sun ce adadin ka iya karuwa lura da yawan wadanda suka jikkata a hare haren.
Ba ya ga fararen hula da suka hallaka, harin ya kuma ritsa da masu farautar gargajiya ‘yan Qabila Dozos wadanda ke tallafawa sojoji a fadan da suke da ‘yan ta’adda a yankin tsakiyar Mali.
Tun daga Octoba mayakan jihadi na kungiyar Katiba Macina suka fara kaddamar da munanan hare hare kan mazauna kauyukan da suka ki yin biyayya ga dokokin da suka kindaya masu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI