Harin ta'addanci a Burkina Faso

Harin ta'addanci a Burkina Faso

An kashe mutane 30 da suka hada da fararen hula 11 sakamakon harin ta'addanci da aka kai a wani kauye a Burkina Faso.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Burkina Faso ta fitar ta ce, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kauyen Markoye da ke iyakar Burkina Faso da Nijar.

An samu arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'addar.

An kashe fararen hula 11, sojoji 15 da mayaka masu goyon bayan gwamnati 4 a arangamar.

 


News Source:   ()