Harin RSF ya kashe mutum tara da jikkata wasu 20 a yammacin Sudan

Harin RSF ya kashe mutum tara da jikkata wasu 20 a yammacin Sudan

Rikicin Sudan ya barke ne a watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan rashin jituwa game da shigar da RSF cikin soja.

Mutum tara ne suka mutu yayin da 20 suka jikkata a yammacin Sudan bayan wani hari da jirgi mara matuki ya kai a safiyar Juma'a a wani asibiti da ke arewacin Darfur, a cewar hukumomi.

Ma'aikatar lafiya ta Sudan ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Al-Fashir, ta kuma dora alhakin harin kan rundunar RSF, wadda ta ce ta harba makaman roka guda hudu daga wani jirgin mara matuki.

Wani kwamitin gwagwarmaya a Al-Fashir da ke da hannu a ayyukan agaji ya ce an kai harin ne kan asibitin na Saudiyya.

Kwamitin ya kara da cewa harin ya tilasta wa cibiyar daina gudanar da ayyukan jinya, yana mai jaddada cewa shi kadai ne asibiti a birnin.

Al-Fashir dai ya sha fama da mummunan rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF tun daga ranar 10 ga watan Mayu. Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jin kai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya barke ne a watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan rashin jituwa game da shigar da RSF cikin soja.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan fiye da miliyan 25 na bukatar agajin jin kai, wanda hakan ya sa rikicin ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren raba mutane da muhallansu da kuma matsalar yunwa, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)