Harin RSF ya kashe mutane 80 a Sudan ana tsaka da tattaunawar sulhu a Geneva

Harin RSF ya kashe mutane 80 a Sudan ana tsaka da tattaunawar sulhu a Geneva

Majiyoyin asibiti a yankin Sennar, sun shaidawa AFP cewar, sun ƙarbi gawarwakin mutane 55 sakamakon harin na ranar Alhamis, yayin da ƙarin wasu 25 suka mutu da safiyar wannan Jumma’a saboda raunin da suka samu.

Tattaunawar wadda ta kunshi masana da wakilan kungiyoyin farar hula, na da nufin cimma tsagaita wuta, da tabbatar da cewa kayan agaji ya kai ga dubban mabukata.

Wakilin Amurka a tattaunawar sulhunta ɓangarori da ke rikicin na Sudan Tom Perriello ya ce ana samun ci gaba a ƙokarin samun hanyoyin shigar da kayan agajin jinkai, duk da cewa gwamnatin sojin Sudan ta ƙauracewa taron na Geneva, amma masu shiga tsakani sun ce lallai akwai tuntuɓa ta waya.

Yau ake shiga kwana na biyu da faro tattaunawar wadda za a shafe kwanaki 10 ana yi a Switzerland, duk da cewa ɓangaren gwamnatin Soji taƙi tura wakilci, amma wakilin Amurka na musamman a Sudan Tom Perriello, ya ce suna tuntuɓar bangaren gwamnati ta waya ko da yaushe kuma ana samun ci gaba.

Ƙasashen Amurka da Saudiyya da kuma Switzerland ne suka ɗauki nauyin tattaunawar, inda ƙungiyar Tarayyar Afirka da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Majalisar Dinkin Duniya ke mara baya tare da zaman shiga tsakanin.

Tun cikin watan Afrilun bara ne sabon yaki ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da tsohon mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo ke jagoranta.

Mummunan rikicin ya haifar da matsancin halin jinkai mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)