Harin masu ikrarin jihadi a Mali ya kashe mutum 70 da jikkata wasu 200

Harin masu ikrarin jihadi a Mali ya kashe mutum 70 da jikkata wasu 200

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa mutanee 77 ne suka mutu, kana 255 suka samu raunuka a harin da aka kai Bamako a ranar Talata.

Zalika, wani bayanin sirri na hukuma da aka tantance sahihancinsa ya ce adadin waɗanda suka mutu ya kai kimanin ɗari, inda ya bayyana sunayen 81 daga cikin su.

Jaridar Le Soir da ake wallafawa a kasar ta ranar Alhamis ɗin nan ya ruwaito cewa a ranar aka yi jana’izar kimanin dakaru masu karɓar soji kimanin 50.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto mahukuntann gwamnatin sojin Mali ba su fitar da ainihin adadin waɗanda su ka mutu  a harin da ƙungiyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai wa ba.

Ƙwararru sun ce harin sshi ne naa farko irin sa a cikin shekaru, kuma ta yi mummmunan tasiri a kan gwamnatin sojin ƙasar.

Ba a cika samun hare-hare a babban birnin ƙasar Mali  kamar yadda ake samu a sauran sassan ƙasar kusan kullayaumin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)