Harin kwanton bauna ya kashe sojojin Nijar 10 a iyakar Mali

Harin kwanton bauna ya kashe sojojin Nijar 10 a iyakar Mali

Lamarin ya faru ne a marecen ranar Litinin, lokacin da ayarin jami’an tsaron ke gudanar da sintiri a wannan yanki da ya yi ƙaurin suna sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, wanda ke kai-da-kawo tsakanin ƙasar ta Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

Kafafen yaɗa labarai sun ce 5 daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu jami’an tsaron jandarma ne, sai kuma na Republican Guards guda 5 da ke aikin sintiri na haɗin gwiwa a tsakaninsu.

Majiyoyi sun ce tuni aka yi jana’izar wasu daga cikinsu a inda lamarin ya wakkana, yayin da aka yi jana’izar gwarwakin jami’an jandarma biyar a birnin Yamai.

Jihar Tillebery da ke yammacin ƙasar, mai iyaka da Mali da Burkina Faso, ita ce mafi fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Sahel da Sahara, kuma sun tsananta kai farmaki kan jami’an tsaro da fararen hula, musamman daga lokacin da ƙasashen Yamma suka janye dakarunsu daga ƙasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)