
Baya ga kisan 'yan ta'addar, an kama wasu tarin makamai, sannan an lalata wasu motocin yaƙi da 'yan ta'addan ke amfani da su.
Sanarwar da ma’aikatar tsaron ƙasar ta fitar ta ce, an kai farmakin kan maɓoyar ‘yan ta’addar ne a wurare da dama da ke jihar Hirshabeelle, a kudu maso tsakiyar kasar ta Somaliya.
Al Shabab mai alaka da Al Qaeda ta kwashe sama da shekaru 15 tana fafatawa da gwamnati, a kokarin da take yi na kafa sabbin dokoki a kasar da ke fama da talauci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dirar mikiyar da sojojin ƙasar suka yi wa mayaƙan, na daga cikin abin da ya basu nasarar kashe da dama daga cikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI