Mutane 6 da suka hada da 'yan sanda 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai kan wata cibiyar jami'an tsaro a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Tashar yada labarai ta Somaliya ta sanar da cewa, an kai harin kunar bakin waken a yankin Waberi na Mogadishu.
Rubutacciyar sanarwar da 'yan sanda suka fitar ta ce,
"A harin kunar bakin wake da aka nufi caji ofis din yankin Waberi shugaban 'yan sandan yankin Ahmed Bashane da mataimakin kwamanda Abdi Basid sun mutu tare da karin wasu fararen hula 6."
Firaminista Huseyin Roble ya fitar da sanarwa ta hafin Twitter inda ya soki harin.