Majiyoyi daga fannin lafiya da suke nemi a sakaya sunansu saboda tsoron abinda ka je ya zo, sun ce harin da aka kaiwa asibitin mai suna Saudi a daren Juma’a, ya lalata ginin baki ɗaya.
Sai dai ya zuwa yanzu, babu masaniya kan wani bangare ne cikin masu rikici da juna ya ƙaddamar da harin.
A cewar majiyoyi daga fannin lafiya, dakarun RSF sun kai hari a ginin asibitin makonni da suka wuce.
Tun watan Afrilun 2023, sojin Sudan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF ke gwabza rikici, inda RSF suka kwace iko da kusan ɗaukacin yankin Darfur.
Dakarun na RSF sun mamaye El-Fasher, babbar birnin Darfur tun a watan Mayu, sai dai har zuwa yanzu basu samu damar kwace iko da birnin ba, saboda dakatar dasu da sojoji ke yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI