Hari a gaban wani gidan cin abinci a Mogadishu

Hari a gaban wani gidan cin abinci a Mogadishu

Mutane 20 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai da wata mota dauke da bam a gaban wani gidan cin abinci a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Manajan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Amin, Abdulkadir Adan ya ba da rahoton cewa mutane 20 sun mutu kuma wasu 30 sun jikkata a harin bam din da aka kai a gaban gidan cin abincin mai suna "Lul Yemen".

An rawaito cewa wani gini a kusa da gidan cin abincin wanda ke kusa da tashar jiragen ruwa ta Mogadishu ya rushe bayan fashewar.

A baya ma wani dan harin kunar bakin wake ya tayar da bam a gaban wannan gidan cin abincin a shekarar 2020 inda mutane suka jikkata a lamarin.


News Source:   ()