Hare-haren ƙungiyar JNIM ya hallaka tarin manyan sojoji a Burkina Faso

Hare-haren ƙungiyar JNIM ya hallaka tarin manyan sojoji a Burkina Faso

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne kan dakarun Sojin na Burkina Faso da ke aiki a birnin Djibo na lardin Soum a Lahadin da ta gabata, kuma ba da jimawa ba ne ƙungiyar ta JNIM ta ɗauki alhakin ƙaddamar da shi, ko da ya ke ba ta bayyana adadin mutanen da ta hallaka ko kuma aka hallaka mata ba.

A gefe guda kamar yadda sashen Faransanci na RFI ya ruwaito ba a iya samun bayanai kan wannan hari daga jami’an gwamnatin ƙasar ta Sahel da ke karƙashin mulkin Soji ba, sai dai ganau sun ce tun da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata ne aka fara jiyo ƙarar harbe-harbe bayan da mayaƙan ƴan ta’addan suka kunno kai daga yankin arewa maso gabashin birnin riƙe da manyan makamai.

Majiyoyi daban-daban da sashen RFI na Turancin faranshi ya tattauna da su, sun bayyana cewa adadin Sojin da suka kwanta dama a harin ka iya zarta 20 galibinsu daga rundunar BIR 22 baya ga mayaƙan sa kai da ke aikin bai wa jama’a kariya wadanda ake kira VDP.

Tsawon shekaru 3 kenan birnin Djibo na fuskantar ƙawanya daga mayaƙan kungiyar ta’addancin ta JNIM ta yadda suke kaddamar da hare-harensu ba kakkautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)