Waɗannan ne dai hare-hare dai na zuwa ne bayan wasu jerin wasu da ƙungiyar ta ADF ta kai a lokacin bukukuwan Kirsimeti, da suka yi sanadin mutuwar mutane 21 a Arewacin lardin Kivu.
Wani jami’i a yankin Samuel Kagheni ya ce ƴan tawayen sun kashe mutane 8 a kauyen Bilendu, wanda bai da nisa da garin Manguredjipa.
Majiyar ta kuma ce an kashe akalla mutane 4 a kauyen Mangoya tare da kona gidaje da wasu wurare a kauyen.
Ƙungiyar ADF da ta samo asali daga Uganda, tun a shekarun 1990 ta ke kashe fararen hula a yankin Arewa maso Gabashin Jamhuriyyar Dimukaradiyyar Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI