Wani jirgin saman sojin Najeriya ya bata bat a lokacin da ya ke bayar da taimako ta sama ga farmakan da ake kai wa 'yan ta'addar Boko Haram a jihar Borno.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar Sojin Saman Najeriya Edward Gabkwet ya fitar ta ce, jirgin saman da aka tura arewa maso-gabas don yakar Boko Haram ya bata.
Sanarwar da aka fitar ta ce, tun ranar 31 ga Maris aka yanke sadarwa da jirgin saman sojin.
Bayan afkuwar lamarin, Shugaban Rundunar Sojn Saman Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya ziyarci yankin.
Amao ya bayyana ana ci gaba da aiyukan nemo jirgin, kuma za su ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya a arewa maso-gabas.