A shekarar 2023 ne, Bankin Duniya ya sanar da cewar kashi daya bisa 4 na jama’ar kasar Ghana na fama da talauci ganin yadda suke rayuwa a kan kasa da dala 2 kowacce rana.
A watan Yulin 2022 kadai, babban bankin Ghana ya yi asarar cedi biliyan 60.8 kwatankwacin dala biliyan 5.3, wanda masana ke ganin abin da ya janyo hakan sake fasalin bashi ne da gwamnatin Akufo Addo ta yi.
A wancan lokacin dai, Ghana mai arzikin zinari da mai da koko, ta kulla yarjejeniya da asusun bayar da lamuni na duniya IMF kan bashin dala biliyan 3, domin taimakawa wajen daidaita tattalin arzikinta.
Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Abdallah Sham-un Bako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI