Dan tawaye Haftar Khalifa na ci gaba da kai mayaka Libiya, a lokacin da yarjejeniyar da aka kulla a ranar 25 ga Disamba karkashin Majalisar Dinkin Duniya kan kafa gwamnatin riko har lokacin da za a gudanar da zabe ta kusa zuwa karshe.
Kakakin Sashen Yada Labarai na Farmakan Sirte da Jufra da dakarun Libiya ke kaddamarwa Janaral Abdulhadi Dirah ya sanar da cewa, wani jirgin dakon kaya da ya tashi daga Siriya ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Al-Abrak da ke karkashin dan tawaye Haftar Khalifa.
Dirah ya sanar da cewa "Duk da tattaunawar siyasa da ake ci gaba da a Swizalan da Morokko, amma dan tawaye Haftar Khalifa na ci gaba da safarar mayaka."
Kuma wani jirgin dakon kaya da ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Abrak ya sauka a filin jirgin sansanin soji da ke Jufra.