
Baya ga kiran ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan na shirin jagorantar taron haɗin gwiwa da ƙungiyar AU a Habasha a ranar Juma’a mai zuwa, don tara wa al’ummar Sudan tallafin kuɗi baya ga na ta taimakon da za ta sanar na Dala miliyan 200.
Sai dai wata majiyar sojin Sudan ta ce ya zama dole ƴan tawayen RSF su janye daga dukkanin birane da yankunan da suka yi wa ƙawanya, kafin a kai ga batun ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta cikin watan na Azumi.
Gwamnatin sojin Sudan dai ta gaggauta yin watsi da tayin na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne, bisa zarginta da taimaka wa ƴan tawayen RSF da makamai, zargin da jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƴan majalisar Amurka suka gaskata, kodayake Daular Larabawan na ci gaba da musantawa.
Har yanzu RSF ba ta ce komai kan tayin tsagaita wutar ba, a yayin da mayaƙanta ke ci gaba da kai farmaki kan birnin al-Fashir, wuri mafi girma da ke ƙarƙashin ikon sojojin Sudan a yankin Darfur.
A can Khartoum babban birnin ƙasar ta Sudan kuwa, sojoji ne ke samun nasara, inda ake sa ran kowane lokaci nan gaba kaɗan za su fatattaki mayaƙan na RSF.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI