Gwamnonin arewa maso-gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan Boko Haram

Gwamnonin arewa maso-gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan Boko Haram

A karon farko gwanoni shida na jahohin Arewa Maso-Gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara daukar matakai masu inganci akan yaki da 'yan ta'addar Boko Haram a yankin.

A kiran da shugaban gwanonin arewa masu gabashin Najeriya gwamnan jihar Borno da Boko Haram ta fi kamari Babagana Zulum ya ratabawa hannu an nuna cewa jami'an tsaron kasar na iya kokarinsu wajen fafatawa da 'yan ta'adda amma kuma akwai matsaloli da nakasu kwarai da gaske.

Kiran ta jaddada cewa ya zama wajibi ga jami'an tsaro su kubutar da yankunan dake cikin mawuyacin hali tare da kuma samar da tsaro a yankunan da ake noma a kasar.

Haka kuma gwamnonin sun nemi a kara yawan sojoji dake yankin a kuma baiwa 'yan sandan yankin ingantattun wadatattun makamai.

Bugu da kari gwamnonin sun nemi a samar da tsaro a yankin tafkin Chadi yankin da kungiyar Boko Haram din ke cin karensu ba babbaka, da hakan ne za'a iya bunkasa samar da ruwan sha a yankin.

Gwamnonin, wadanda suka amince suka aminta akan hadin kai domin bunkasa fannonin masana'antu, ma'adinai, mai, gas da noma don ci gaban yankin, sun ba da sanarwar cewa sun goyi bayan shawarar sauya tsarin Almajiri zuwa ilimin addinin Musulunci da na Yamma, lamarin da ya haifar da manyan matsalolin tsaro da matsalolin tattalin arziki a Najeriya.

Gwamnonin da suka yi wannan kiran sun hada da gwanonin jihohin Adamava, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

 


News Source:   ()