Gwamnatin Sudan za ta mika Al-Bashir ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

Gwamnatin Sudan za ta mika Al-Bashir ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

Ministar Harkokin Wajen Sudan Maryam Sadik Al-Mahdi ta bayyana cewa, Majalisar Ministoci Kasar ta dauki matakin mika tsohon Shugaban Kasar Umar Al-Bashir da wasu tsaffin jami'an gwamnatinsa ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).

Kamfanin dillancin labarai na Sudan (SUNA) ya bayar da labarin cewa, Al-Mahdi da ta gana da Babban Mai Gabatar da Kara na ICC Karim Han a Khartoum Babban Birnin Sudan ta bayyana a shirye suke su hada kai da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya don yin adalci ga wadanda yaki ya rutsa da su a yankin Darfur.

Ministar ta ce, Sudan ta shirya don mika mutanen ga ICC, kuma za su yi aiki da Yarjejeniyar Rum.

Ta ce, za a kammala amincewa da matakin a wajen Taron Majalisar Ministoci da ta Mulkin Kasa.


News Source:   ()