Sauye-sauyen da shuagaban mulkin sojin na Sudan ya bukaci a yi, zai ba shi cikakkiyar damar naɗawa da cire duk wanda ya ke bukata ciki har da Firaminista a kasar.
Hakanan sauyin zai ba da damar ƙara adadin mambobin zartaswar ƙasar daga biyar zuwa tara.
Sannan mutane ukun da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ta juba peace agreement zasu ci gaba da zaune matsayinsu a yayin da shi kuma zaii naɗa wasu mambobi 6.
Batun gyaran da wasu ‘yan siyasa dake da alaƙa da sosjojin ƙasar suka shirya, ya samu ne bayan da aka bukaci a gudanar da kwaskwarimar yarjejeniyar da aka shirya ta shekarar 2019.
Sauye-sauyen zai kawar da duk wani tsari na ƙungiyar ‘yancin samar da sauyi da kuma dakarun ɗaukin gaggawa ta RSF, a yayin da za a bar wakilan da suka rattaba hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta juba akan aikinsu.
Al-Burhan ya ba da wannan sanarwar sauye-sauyen ne a yayin wani bikin mata da gudana a Omdurman a wannan mako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI