"An nada Manjo Janar Abdoulaye Maïga a matsayin sabon Firaministan wannan kasa ta Mali," in ji sakataren fadar shugaban kasa, Alfousseyni Diawara ta kafar gidan talibijin din gwamnati.
Tun da farko dai ya kasance ba ya cikin kanar-kanar din da suka hambarar da gwamnatin farar hula a watan Agustan 2020.
An haife Janar Abdoulaye Maiga a ranar 12 ga Mayu 1981,ya kuma rike mukamin hafsan sojan Mali mai magana da yawun gwamnati.
An nada shi Firaministan Mali na wucin gadi a ranar 21 ga Agusta 2022.
Janar Abdoulaye Maiga ya kasance a rundunar jandarma wanda rundunar soja ce mai aikin tabbatar da doka a tsakanin farar hula kuma wani bangare na sojojin kasar ta Mali.
Sabon Firaministan Mali,Janar Abdoulaye Maiga ya yi nazarin diflomasiyya da dokokin kasa da kasa a Algiers na kasar Algeriya.
Ya karanci manufofin tsaro da tsaro na kasa da kasa a birnin Paris na kasar Faransa, kana ya na da digiri na uku a fannin tsaro na kasa da kasa daga Jami'ar Jean Moulin Lyon 3.
Tarihi ya nuna cewa sabon firaminista ya yi aiki da Cibiyar Gargaɗi na Farko kan Kariya da Ta'addanci a Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka, ECOWAS.
Ya yi aiki a matsayin ɗan sanda da rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ,MONUSCO a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
A cikin watan Yunin 2021 aka nada shi a matsayin ministan Ma'aikatar Gudanarwa da Rarraba yankuna, kuma a ranar 1 ga Disamba 2021 aka nada shi mai magana da yawun gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI