Taron majalisar ministocin da aka yi a fadar shugabancin kasar, ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar, daidai da 12 ga Afrilin 2025.
Kwace mulkin kasar da shugaban gwamnatin rikon kwarya, Brice Oligui Nguema ya yi, na daga cikin juyin mulki har sau takwas da aka yi daga Yammaci zuwa Tsakiyar Afirka tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, abin da ya kawo karshen mulkin iyalan gidan hambararren shugaba Ali Bongo.
A watan Nuwamba ne, al’ummar suka amince da sabon kundin tysarin mulkin kasar da aka gudanar da zaben raba gardama a kansa.
Sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar wa’adin shekara bakwai-bakwai sau biyu akan mulki, amma babu firaministan ko kuma batun mika mulki kai tsaye ga wani, sai dai a gudanar da zabe.
Sai dai ana fargabar gwamnatin sojin za ta yi amfani da wannan damar, wajen ci gaba da rike madafun iko a kasar.
Sabuwar dokar ta bawa jami'an soji damar tsayawa takara a zabukan kasar, wanda hakan ke nufin Nguema, wanda ya bayyana aniyarsa karara, na iya ci gaba da rike mulkin kasar, amma karkashin gwamnatin farar hula.
Kasar da ke tsakiyar Afirka mai arzikin man fetur, ta kasance karkashin mulkin gidan iyalan Bongo har tsawon shekaru 55, amma sojojin sun kawo karshen mulkin gwamnatin a watan Agustan 2023.
Ali Bongo ya mulki kasar har tsawon shekaru 14, wato zuwa lokacin da aka hambarar da gwamnatinsa, bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da 'yan adawa suka ce an tafka magudi.
Bongo ya karbi ragamar kasar bayan mutuwar mahaifinsa, Omar Bongo, wanda ya mulki kasar tsawon sama da shekaru 41.
'Yan adawa da kuma sojojin da suka yi juyin mulkin, sun zargi gwamnatin Bongo da rashin gudanar da mulki bisa tsarin doka hadi da cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI