Gwamnatin Senegal za ta gabatar da tsarin samar da tallafi don rage radadi yan kasar

Gwamnatin Senegal za ta gabatar da tsarin samar da tallafi don rage radadi yan kasar

Shugaba Bassirou Diomaye Faye da Firaministansa Ousmane Sonko a watan Maris din da ya gabata sun dau alkawura da cewa za su tabbatar da adalci a bangren da ya shafi zamantakewa, samun 'yancin kai da kuma samarwa yan kasar da ababen more rayuwa ga baki daya.

Bayan rantsar da shi a watan Afrilu, Faye ya bukaci Sonko ya gudanar da cikakken nazari kan halin da ake ciki na hada-hadar kudi na kasar.

A yau Alhamis ne gwamnatin kasar za ta soma aiwatar da wasu daga cikin alkawuran da ta dauka na raba hannun jarin kamar dai yada sanarwa daga ofishin firaminista ta tabbatar.

Firaministan Senegal Ousmane Sonko Firaministan Senegal Ousmane Sonko © SEYLLOU / AFP

 Bikin, da aka gayyaci manema labarai, zai zama wata dama ta tattauna kurakuran da aka gano "da kuma matakan dakile wannan lamarin da aka gada", in ji firaministan kasar ta Senegal Ousmane Sonko.

 Har ya zuwa kwanan nan majalisar dokokin da 'yan adawa ke da rinjaye ta kawo cikas ga matakin gwamnati. A tsakiyar watan Satumba ne Shugaban kasar Bassirou Faye ya rusa majalisar dokokin kasar tare da sanya sabbin zabukan ‘yan majalisar dokoki a ranar 17 ga watan Nuwamba, inda ya nemi aiwatar da manufofinsa.

 Sannan ya yi magana game da "mummunan tabarbarewar" kudaden gwamnati.Bayan wata ziyara da ma'aikatan asussun bayar da lamuni na IMF suka kai kasar Senegal dake yammacin Afirka, asusun ya ce yana sa ran yanayin kasafin kudin kasar "zai tabarbare sakamakon karancin kudaden shiga da kuma karin kudaden da ake kashewa kan tallafin makamashi da kudin ruwa".

Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko AP - Sylvain Cherkaoui

 Don rage basussukan jama'a,asusun lamuni na  IMF ya bukaci gwamnatin Sonko da ta aiwatar da matakan "da suka hada da daidaita harajin haraji da kuma kawar da tallafin makamashi marasa niyya da tsada.

Sanarwar da ofishin Sonko ya fitar ta ce, an gudanar da bitar halin da kasar ke ciki ne a daidai lokacin da aka tsara wani sabon tsarin tattalin arziki. Sanarwar ta ce, shirin gwamnati mai taken "Senegal 2050 - Ajandar kawo sauyi na kasa" an tsara shi ne domin samar da dauwamammen sauyi ga tattalin arzikin kasar Senegal da gina kasar Senegal mai cikakken 'yanci, adalci da wadata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)