
Gwamnatin Nijar ta ɗauki matakin ne bayan taron majalisar sojojin ƙasar, wadda ta bayar da umarnin kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyar agajin ta Red Cross.
Wasu majiyoyi dai na cewa akwai yiwuwar ragowar ƙasashen sabuwar ƙungiyar AES, wato Mali da kuma Burkina Faso su ɗauki irin wannan mataki.
Wannan na zuwa ne kwanaki ƙalilan, bayan cikar wa’adin ficewarsu daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a makon da ya gabata.
A shekarar 2023 ne, gwamnatin sojin Nijar ta bukaci ficewar wakilan Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar, bisa zargin kebe ƙasar daga cikin ƙasashen da suka halarci babban taron Majalisar, wanda aka yi a birnin New York na Amurka.
Cikin watan Yulin shekarar ne, sojoji suka hambarar da shugaba Mohammed Bazoum daga karagar mulkin kasar, tare da rushe majalisar gudanarwa, inda aka ayyana Janar Abdourahamane Tiani, a matsayin wanda zai rike mukamin gwamnatin rikon kwarya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI