Gwamnatin Nijar ta dakatar da tashar BBC na tsawon watanni uku

Gwamnatin Nijar ta dakatar da tashar BBC na tsawon watanni uku

Majalisar sojin kasar ta bakin ministan sadarwa, Sidi Mohamed Raliou ya bayyana cewa matakin zai fara aiki kama daga jiya alhamis a duk fadin kasar ta Nijar.

Gwamnatin mulkin soja ta CNSP ta haramtawa kafafen yada labarai na yammacin duniya da dama tun bayan da ta kwace mulki bayan juyin mulki a watan Yulin 2023. Shahararrun shirye-shiryen BBC da suka hada da na harshen Hausa ana watsa su a Nijar ta hanyar abokan aikin rediyo na cikin gida.

An dakatar da gidajen rediyon Faransa guda biyu, Rediyo France Internationale (RFI) da tashar talabijen na France 24,tun watan Agusta 2023.

Kasar Nijar tsawon shekaru dai ta sha fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru daga kungiyoyin masu da'awar jihadi masu alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS. Hare-haren masu jihadi sun yi sanadiyar kashe akalla fararen hula da sojoji 1,500 a kasar a cikin shekarar da ta gabata, a cewar kungiyar sa ido kan rikice-rikice ta ACLED  fiye da ninki biyu na mutane 650 da aka kashe daga Yuli 2022 zuwa Yuli 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)