Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta ce ta bankado ma’aiktan bogi sama da dubu 3 wadanda ake biya albashin miliyan 540 kowane wata cikin asusun gwamnati.
Zainabu ,ta ce wani bincike da aka gudanar tsakanin watan Yuli zuwa Augustan wanan shakara ya gano yadda ake zurare biliyoyin kudi daga asusun bital malun na kasa domin biyan ma’aikatan da babu su a zahiri.
Rahoton binciken ya ce a watani uku farkon shekara 2022 biliyan 7,7 aka kashe wajan biyan fanshon ma’aikata sabanin biliyan 12,8 da aka kashe a watanin uku farkon shekara 2023 duk da raguwa masu tafiya ritaya da aka samu saka makon tsawaita lokacin zuwa ritaya da akayi da shekaru 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI