Gwamnatin Najeriya ta kori ma'aikata masu riƙe da digiri ɗan Kwatano da Togo

Gwamnatin Najeriya ta kori ma'aikata masu riƙe da digiri ɗan Kwatano da Togo

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daraktan yaɗa labaran ofishin sakataren gwamnatin ƙasar, Segun Imohiosen ya ce matakin ya shafi ma’aikatan da ke aiki tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

A watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin ta sanar da cewa iya jami’o’i 8 na ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin ƙadai ta sahale su bai wa ƴan Najeriya shaidar kammala karatun digiri.

Wannan dai ya biyo binciken ƙwa-ƙwaf da jaridar Daily Nigerian ta yi wanda ma’aikacinta ya yi basaja da sunan yana neman shaidar karatun digiri , kuma ya samu cikin watanni 2 daga jami’ar Benin, har ma ya yi amfani da shi wajen yin aikin yiwa ƙasa hidima na NYSC.

Lamarin da ya bankaɗo wannan badakala, ya haifar da cece-kuce a sassan ƙasar, har ma gwamnatin Najeriyar ta haramta halascin shaidar kammala karatu daga jam’o’in Benin da Togo tare da kafa kwamitin bincike kan batun.

Tsohon ministan ilimin Najeriya a lokacin, Tahir Mamman ya bayyana cewa sama da ƴan Najeriya 22,500 ne ke da shaidar kammala karatun digiri daga Benin da Togo, kuma an soke halascinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)