Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga da 'yan ta'addar Boko Haram da ke kasar ba.
Mai Baiwa Shugaban Najeriya Shawara Kan Sha'anin tsaro Babagana Monguno ya shaida cewa, gwamnati ba za ta yi sulhu da 'yan ta'adda da 'yan bindiga da ke yawan kai hare-hare a kasar ba.
Monguno ya ce, sulhu da 'yan ta'adda na nufin gazawa da raunin gwamnati, kuma sun zabi amfani da dukkan karfi wajen murkushe 'yan ta'adda da 'yan bindigar.
Shugaban najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa 'yan bindigar wa'adin watanni 2 da su mika makamansu.