Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zarge-zargen shugaban mulkin sojin Nijar

Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zarge-zargen shugaban mulkin sojin Nijar

Ministan yaɗa labarai na Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wata takadda da ya fitar a yammacin yau a matsayin martani kan wata hira da shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar Tchiani ya yi. inda ya zargi Najeriya da ƙoƙarin kawowa ƙasar tsaiko.

Sanarwar ta ce shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ya nuna shugabanci abin koyi tare da barin ƙofa a buɗe ga Jamhuriyar Nijar duk kuwa da halin da ake ciki na juyin mulki a ƙasar.

Najeriya ta ce a shirye take wurin tabbatar da kyakykyawar alaƙa da zaman lafiya da fahimtar juna da kuma kyautata alaƙar diflomasiyya mai tsohon tarihi dake tsakaninta da Nijar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sojin Najeriya haɗin gwiwa da abokanan hulɗarta na samun nasara sosai wurin yaƙi da ta’addanci a yankin, don haka abin mamaki ne ace ƙasar za ta haɗa kai da wata ƙasar waje wurin kawo tsaiko ko rashin zaman lafiya a makwaftan ƙasashe.

Gwamnatin Najeriyar ta ce babu wani jami’inta da ya taɓa goyan bayan ƙungiyoyin ƴan ta’adda ko wata kungiyar ƴan ta’adda wurin kaiwa Nijar hari.   

Gwamnatin ƙasar ta ce Najeriya tana tsaye kan kafafunta da cikakken iko kan ƙasar. kuma ba ta taɓa bai wa wata ƙasa dama ko iko na kafa sansanin soji a cikinta ba, sabanin abin da wasu ƙasashe ke yi. Wannan na nuna yadda shugabancin Najeriya ya yi tsayuwar daka wurin tabbatar da ƴancin ƙasar.

Dangane da zargin da shugaban ƙasar Nijar ya yi cewa ana shirin kawowa bututun mansu da ayyukan gona tazgaro  gwamnatin ta ce kwata-kwata ba gaskiya bane.

Gwamnatin Najeriya ta ce waɗannan zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani ya yi tamkar kawar da hankalin jama'a ne daga gazawar da mulkinsa tun bayan da ya jagoranci juyin mulki. Gwamnatin ta buƙaci Jamhuriyar Nijar ta mayar da hankali wurin tattaunawa da haɗa kai maimakon zarge-zarge marasa tushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)