Gwamnatin Libiya ta bayyana janye Ministan Harkokin Wajenta daga wakilcin da yake yi a Tarayyar Kasashen Larabawa sakamakon halin munafurci da fuska biyu da Tarayyar ta nuna musu.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Libiya ta fitar ta ce "Libiya ta janye wakilinta daga Tarayyar Larabawa saboda halin fuska biyu da Tarayyar ta nuna. Tun shekarar da ta gabata Libiya ta bukaci a gudanar da taron Kasashen Tarayyar duk da cewar an samu adadi mai yawa da yake goyon baya, amma aka ki yin hakan."
Sanarwar ta rawaito Wakilin Libiya a Tarayyar Larabawa Salih Al-Shemahi na cewar "Dakarun Libiya sun kassara 'yan ta'adda mabiya Haftar, sun kwace garuruwan da ke hannunsu. Na karshe shi ne garin Terhune. Bayan an kawar da hare-haren da ake kai wa a Tarabulus sai ga kasashen da ke goyon bayan Haftar na kira da a tsagaita wuta."
Semahi ya kuma soki kasashen da ke goyon bayan Haftar da ke cin karensa babu babbaka a Kudancin Libiya.