Zanga-zangar watan yuni ya girgiza hukumomin wannan kasa ta Kenya, inda matasa da dama suka bijerwa umurnin Shugaban kasar William Ruto a kan manufofinsa da suka jibanci tattalin arziki.
Sakonnin daga shugabanin matasa da kungiyoyi na kira ga jama’a na ganin sun fito a yau alhamis a wata sabuwar zanga-zanga wadanda aka yiwa lakabi da "Nane Nane" da ya zo dai dai da wannan rana ta 8 ga Agusta.
Da yammacin jiya laraba, mukaddashin shugaban 'yan sanda Gilbert Masengeli ya yi gargadin cewa "masu aikata laifuka" na shirin kutsawa cikin zanga-zangar kuma ya ce ya zama wajibi jama’a su kauracewa wasu wurare yayin wannan zanga-zanga kamar filin jirgin sama na kasa da kasa da kuma gidan gwamnati, da gidan shugaban kasar. Ya kara da cewa an tura isassun jami'an tsaro.
'Yan Sandan Kenya yayin daƙile jeriin gwanon masu zanga-zanga da ke ƙoƙarin miƙa takardar koke ga gwamnati a birnin Nairobi. REUTERS - Thomas MukoyaIndan aka yi tuni , zanga-zangar lumana da farko a ranar 25 ga watan Yuni, ta kasance wani lokaci da aka shiga rudani a kasar ta Kenya,wanda ya kai jami’an tsaro amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu bore a fadain kasar musaman a babban birnin kasar Nairobi.
Masu zanga-zanga a Nairobi na kasar Kenya REUTERS - Monicah MwangiA wasu rahotanni daga kungiyoyin kare hakkin bil adama, akalla mutane 60 aka kashe tun watan Yuni, wasu da dama kuma sun bata.Rahotannin na zargi 'yan sanda da yin amfani da karfin tuwo kan jama’a. Wannan zanga-zangar ta sa Shugaban kasar Willima Ruto janye kudurin kasafin kudin da ake ta cece-kuce da shi wanda ya tanadi sabbin haraji da dama, ya kuma kori kusan dukkanin jami’an gwamnatinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI