Gwamnatin Kenya na shirin dawo da batun da karin harajinda ya janyo da tashin hankali

Gwamnatin Kenya na shirin dawo da batun da karin harajinda ya janyo da tashin hankali

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi tir da cin zarafi ba bisa ka'ida ba da aka yi wa jama’a yayin wadannan tarukan, da mutuwar mutane fiye da 60 da kuma kama wasu da dama ba bisa ka'ida ba.

Gwamnati, na fama da bashin kusan dala biliyan 80, yanzu tana shirin sake bullo da wani sabon tsarin haraji don kara yawan kudaden shiga na kasafin kudinta, da suka hada da karin harajin VAT da kuma karin haraji kan fannin dijital.

Wannan yana nufin musamman cewa masu zaman kansu da ke aiki a cikin isar da abinci da bangaren sufuri, tushen samun kudin shiga da ya karu sosai a cikin 'yan shekarun nan, za su kasance ƙarƙashin harajin kuɗin shiga a karon farko.

Shugaban kasar Kenya William Ruto Shugaban kasar Kenya William Ruto © Thomas Mukoya / REUTERS

Wannan sabon tsarin haraji, waɗanda dole ne a aika da su ga majalisa nan ba da jimawa ba, an sanar da su dalla-dalla a cikin wani bayanin gwamnati da wasu kafofin watsa labarai na cikin gida suka buga a yau Juma'a.

Wadannan harajin da aka gabatar na kara hadarin haifar da sabon rikici a kasar da kashi uku na al'ummar kasar ke rayuwa kasa da kangin talauci.

Zanga-zangar direbobin kasar Kenya Zanga-zangar direbobin kasar Kenya © Gaëlle Laleix

A wani jawabi da ya yi, shugaba William Ruto ya ce ci gaban Kenya ya kasance a baya bayan shekaru goma saboda kasar ta gaza wajen kara kudaden haraji.

"Saboda haka, ba mu da albarkatun da ake bukata don ci gaba," in ji shi, yana mai da hankali kan matasa 850,000 da ke shiga kasuwannin kwadago a kowace shekara kuma suke gwagwarmayar samun aikin yi.

Sai dai bai yi magana musamman kan sabbin kudurorin ba, amma ya ce gwamnati na da burin kara kudaden haraji daga kashi 14% na GDP zuwa kashi 22 cikin dari cikin shekaru goma. "Dole ne matakan harajinmu su kasance masu gaskiya kuma duk wanda ya cancanta dole ne ya biya," in ji shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)