Cikin wata wasika da ya aike wa gwamnonin jihohin ƙasar goma, ministan cikin gidan ƙasar Paul Biya Paul Atanga Nji, ya ce tattaunawa rashin lafiyar shugaban babban laifi ne da ya shafi tsaron ƙasa, don haka gwamnoni su ɗauki matakin da ya dace kan duk wata kafa da saɓa umurnin.
“Shugaban ƙasa shine babbar jagoran jamhuriya, kuma tattaunawa kan halin da yake ciki lamari ne da ya shafi tsaron kasa,”
Biya, wanda shi ne shugaban da ya fi tsufa a duniya, an daina jin ɗuriyarsa tun a farkon watan Satumba, lamarin da ya ƙara rura wutar jita-jitar da ake yaɗawa a yanar gizo cewa rashin lafiyar sa ya tabarbare.
Biya ya shafe fiye da shekaru 41 a matsayin shugaban ƙasar Kamaru, kuma shine na biyu mafi daɗewa a nahiyar Afirka bayaga Teodoro Obiang Nguema Mbasogo mai shekaru 82, wanda ya kwashe shekaru 45 yana mulki a Equatorial Guinea.
An ɗaina jin ɗuriyarsa
An yi wa Biya ganin ƙarshe a taron ƙasashen Afirka da China aka yi a birnin Beijing a watan jiya.
Bai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a birnin New York ba, ko kuma taron ƙasashe masu magana da harshen Faransanci a birnin Paris.
Ofishin shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa ranar Talata yana mai cewa Biya na cikin koshin lafiya, inda ya yi Allah-wadai da jita-jitar akasin haka a matsayin bayanan ƙarya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI