Gwamnatin Kamaru ta ƙaryata jit-jitar mutuwar shugaba Paul Biya

Gwamnatin Kamaru ta ƙaryata jit-jitar mutuwar shugaba Paul Biya

Shugaba Paul Biya mai shekaru 91, ya bar ƙasar ne tun  ranar 2 ga watan Satumba domin halartar taron Afirka da China da aka gudanar daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba.

Tun daga lokacin ne aka daina jin ɗuriyarsa, inda hatta babban taron Majalisar Dinkin Duniya da na kasashen Francophonie da ya saba halarta kuma aka sanar zai je ma, wakilci aka tura.

Haka zakalika, Paul Biya bai halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin Kamaru da aka gudanar kwanaki goma da suka wuce ba, kamar yadda ya saba yi.

Rashin halartan wadandan taruka ya jefa ƴan kasar Kamaru cikin rudani, inda aka fara yada jita-jita daga ciki da wajen ƙasar masamman a kofofin sada zumunta na zamani cewa shugaban ƙasar na cikin mawuyacin hali kwance awani abisiti a ƙasar Swizland.

Shiru da gwamnati da ma jam’iyyar RDPC mai mulki suka yi na dogon lokaci ya ƙara haifar da ruɗani a zukatan yan kasar, abin da ya sa ma wasu shugabannin jam’iyyun adawa suka bukaci a bayyana musu halin da shugaban ƙasar ke ciki.

Cikin wadanda suka fito fili suka bukaci ƙarin haske kan halin da shugaba Paul Biya ke ciki, harda ficeccen lauya kuma ɗan takarar neman shugabancin ƙasar a jam’iyyar adawa Christian Ntimbane da ya rubuwata daraktan fadar shugaban ƙasar Samuel Mvondo Ayolo wasika.

Da yammacin wannan Talata, hukumomin ƙasar suka mayar da martani bayan da wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo da ke watsa shirye-shiryenta a ƙasashen waje ta sanar da mutuwar shugaban da ya kwashe shekaru 42 yana mulkin ƙasar.

Jacques Fame Ndongo, sakataren sadarwa kuma memba a jam’iyya mai mulki ne ya fara ƙaryata batun,

 “Wannan labari ne marar tushe, don haka masu kishin ƙasa da abokan huldarmu ku kwantar da hankalinku”

Sa'i kuma, babban sakataren jam'iyyar, Grégoire Owona, kuma ministan Kwaɗago, shi ma ya mayar da martani, ya na mai gargadi masu neman haifar da hargitsi.

"Wadanda suke kokarin yaudarar jama'a ta hanyar sanar da mutuwar shugaban kasar Kamaru, za su girbi abin da suka shuka kan wannan ƙazafi"

Daga bisani Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar kuma ministan sanarwa Rene Emmanuel Sadi ya ƙarya zargin a hukumace, inda ya ce rahotannin da ake yadawa a kafofin sada zumunta tare da wasu tashoshin yada labarai ba wani abu bane sai labarin kanzon kurege.

Mista Sadi ya ce shugaba Paul Biya na nan a raye cikin koshin lafiya, sabanin jita jitar da ake yadawa cewar ya mutu kuma yana cikin koshin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)