
Bayan 'yan kwanaki da ƙwace birnin Goma da ke makwabtaka da arewacin Kivu, M23 ta ayyana cewa an tsagaita buɗe wuta, domin bayar da damar kai agaji ga mutanen da rikicin ya ɗaiɗaita.
'Yan tawayen da ke fito-na-fito da gwamnati, sun sanar da cewa basu da wani shirin kwace ikon yankin Bukavu, da kuma garuruwan da ke yankin.
Majiyoyin tsaro da na ƙungiyoyin bayar da agaji a gabashin Jamhuriyar Congo, sun ce ‘yan tawayen M23 tare da haɗin gwiwar sojojin Rwanda,, sun ƙaddamar da sabon farmaki kan sojojin ƙasar ta Congo, lamarin da ya basu damar ƙwace iko da garin Nyabibwe, mai nisan kilomita kimanin 100 daga birnin Bukavu.
Bayanai sun ce ƙazamin faɗa ya ɓarke tsaknain sojojin Jamhuriyar Congon da kuma hadin gwiwar mayaƙan M23 da sojin Rwanda ne da sanyin safiyar yau Laraba, kwana guda bayan sanarwar tsagaita wutar da ‘yan tawayen suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI