Gwamnati Senegal za ta kawo karshen dogaro da kasashen ketare

Gwamnati Senegal za ta kawo karshen dogaro da kasashen ketare

A wannan mataki,gwamnatin kasar ta Senegal ,tun bayan nasarar da Bassirou Diomafaye ya samu a watan Afrilu,ya na da niyar kawo karshen dogaro da kasashen ketare kamar dai yada aka saba a yan shekaru da suka gabata.

Shugaban Senegal  Bassírou Diomaye Faye Shugaban Senegal Bassírou Diomaye Faye AFP - CHARLY TRIBALLEAU

Musaman a bangaren da ya shafi karbar basussuka, a maimakon hakan gwamnatin Senegal na sa ran dogaro da albarkatun cikin gida da wasu gundumuwar yan kasar ga baki daya a cewar Firaminista Ousmane Sonko a jiya Juma'a.

Firaministan kasar ta Senehgal Ousmane Sonko y ana mai bayyana babu abinda ya dace da kasashen Afrika fiye da tsarin kasar Japan,inda ya karasa da cewa,ƙasashenmu (Afrika) mun gwammace a koya mana yadda ake kamun kifi maimakon a ci gaba da ba mu kifi.

Firaministan Senegal Ousmane Sonko Firaministan Senegal Ousmane Sonko © SEYLLOU / AFP

Senegal na da arzikin albarkatun kasa da suka hada da man fetur da iskar gas, ma'adanai da kifaye, amma har yanzu tana daya daga cikin kasashe mafi karancin ci gaba a Duniya.

A lokacin da Firaministan kasar ke maga a kai ,bai gabatar da jadawalin sa ba,wandada ke dauke da manufofinsa ba, watanni shidan farko da gwamnatin ta yi kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)