Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya

Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya

An sanar da cewa a harin da kungiyar ta'aadar Boko Haram ta kaiwa tawagar gwamnan Borno Babagana Zulum mutun 15 sun rasa rayukansu.

Kamar yadda kafafen yada labaran kasar  suka sanar a yayında gwamna Zulum ke ziyarar wadanda suka rasa matsugunansu a yankin Baga an kaiwa tawagarsa hari. 

A harin hadi da yan sanda 7 da sojoji 3 mutum 15 sun rasa rayukansu inda kuma aka bayyana raunanan wasu da dama.

An dai sanar da cewa duk da dai gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya ba tare da ya samu ko rauni ba a harin, motar da yake ciki ta barnatu. 

A Najeriya dai daga shekarar 2000 kawo yanzu Boko Haram ta hallaka fiye da mutum dubu 20.

 

 


News Source:   ()