
Ga dukkanin alamu dai shugaba Emabalo bai damu da caccakar da ake yi masa ba, la’akari da aniyarsa da ya bayyana ta ci gaba da zama kan mulkin Guinea-Bissau har zuwa lokacin da za a zaɓi magajinsa, lamarin da ya ƙara fusata ɓangaren ‘yan adawar da tsohon Fira Minista Domingos Simoes Pereira ke jagoranta.
A cewar ‘yan adawar, ya zama dole shugaba Umaro Sissoco Embalo ya sauka daga mulki a ranar alhamis mai zuwa wato 27 ga watan nan na Fabarairu, domin a lokacin wa’adinsa zai ƙare, duk da cewa a bayan kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukuncin cewa sai a ranar 4 ga watan Satumban shekarar nan wa’adin shugaban zai ƙare.
A watan Disambar shekarar bara ta 2024 yakamata a ce zaɓen shugabancin ƙasar ya gudana, amma shugaba Umaro Sissicko ya sanar da ɗage zaɓen a ranar 4 ga watan Nuwamba, ‘yan kwanaki bayan yunƙurin juyin mulkin da gwamnatinsa ta ce an yi.
Sau huɗu aka taɓa yin juyin mulki a Guninea-Bissau yayin da aka yi yunƙurin yin juyin mulkin fiye da sau 10, daga lokacin da ƙasar ta samu ‘yan ci kai daga Portugal a shekarar 1973 zuwa yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI