Guelleh ya lashe zaben shugaban kasar Djibouti karo na biyar

Guelleh ya lashe zaben shugaban kasar Djibouti karo na biyar

Shugaban kasar Djibouti da ke gabashin Afirka  Ismaïl Omar Guelleh, dake kan gado na jam'iyyar People's Movement for Progress (RPP),  ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

A zagayen farko na zaben da aka gudanar jiya a Djibouti, kimanin masu kada kuri’a dubu 215 ne suka je akwatin jefa kuri’a.

A zabukan da ‘yan adawa suka kaurace wa bisa hujjar cewa ba'a tsara shi bisa adalci da inganci ba , Shugaba Guelleh mai shekaru 73  ya fafata da dan takaran mai zaman kasansa Zekeriya İsmail Farah.
Ministan cikin gida Mumin Ahmed Sheikh ya fada wa kafar watsa labarai ta RTD cewa, an sake zaben Guelleh da kashi 98.58 na kuri’un, a cewar sakamakon da ba na hukumance ba.

Guelleh ya samu kuri’u dubu 167 da 535, sannan abokin hamayyarsa daya tilo, Farah, ya samu kuri’u kasa da 5000.

Da wadannan sakamakon, an zabi Shugaba Guelleh na yanzu karo na 5 a jere bayan zabukan shekarar 1999, 2005, 2011 da 2016 da ya lashe.

Wanda ya lashe zaben, Shugaba Ismail Umar Guelleh, ya fada a shafinsa na Twitter da cewa,

"Na gode da amincewar ku. Na gode Djibouti. Bari mu ci gaba tare."


News Source:   ()