Gudun hijira a Burkina Faso ya karu da kaso 80 cikin dari

Gudun hijira a Burkina Faso ya karu da kaso 80 cikin dari

Gudun hijira a Burkina Faso da ke yammacin Afirka ya karu da kaso 80 cikin dari.

A shekarar 2019 kusan mutane dubu 560 suka yi gudun hijira a cikin kasar, a shekarar 2020 kuma adadin ya kai miliyan daya.

An samu mafi yawan gudun hijira a arewacin kasar. Kaso 54 na wadanda suka yi kaura sabo rashin abinci, matsuguni da kayan more rayuwa 'yan kasa da shekaru 15 ne.

Ana yawan samun hare-haren ta'addanci a yankunan arewaci da gabashin Burkina Faso da ake kira yankin Sahel da ke iyaka da Nijar da Mali.

Tun daga shekarar 2015 zuwa yau an kashe mutane sama da 900 a yankin sakamakon hare-haren ta'addanci.


News Source:   ()