Goita ya yiwa kansa da wasu muƙarrabansa ƙarin girma a rundunar Sojin Mali

Goita ya yiwa kansa da wasu muƙarrabansa ƙarin girma a rundunar Sojin Mali

Taron wannan ƙarin girma da ya gudana jiya Laraba a birnin Bamako fadar gwamnatin ƙasar, bayanai sun ce ya samu halartar biyu kadai daga cikin tsaffin shugabannin ƙasar, ƙarin girma da masana ke ganin manuniya ce da ke tabbatar da cewa jagoran Sojin ba shi da nufin miƙa mulki ga farar hula a nan kusa.

A shekarar 2020 ne Kanal Assimi Goita ya jagoranci wani juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula a ƙasar ta yammacin Afrika.

Tun farko majalisar ministocin shugaba Goita ce ta sanar da shirin ƙarin girman wanda ya shafi shugaban da kuma wasu manyan Sojin ƙasar 5 da aka yiwa ƙarin girma zuwa laftanal janar.

A cewar Rida Lyammouri babban jami’i a cibiyar da ke sanya idanu a shugabanci da ke Morocco, matakin mahukuntan na Mali na nuna cewa za a ɗauki tsawon lokaci gabanin komawar mulki hannun farar hula a ƙasar.

Har kawo yanzu dai Sojin Mali basu sanya ranar gudanar da zaɓe ba yayinda suka katse hulɗa tsakaninsu da dukkanin wasu ƙasashe ko manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ka iya tilasta musu kiran zaɓe, a wani yanayi da ake ci gaba da ganin hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)